Dubban Jama'a na tsere wa garin Wukari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mazauna Wukari na guduwa zuwa garuruwan dake makwabtaka da su

Rahotanni daga jihar Taraba dake arewa maso gabashin Nijeriya na cewa dubban mutane na kara yin kaura daga garin Wukari, bayan wani kazamin tashin hankali da aka yi a garin a makon jiya.

Wasu bayanai dai na cewa mafiya yawan jama'ar garin sun kaurace wa garin, inda suka fantsama zuwa wasu kananan hukumomin dake cikin jihar ta Taraba, da kuma wasu jihohi masu makwabtaka da jihar.

To sai dai kuma mahukunta a jihar na cewa sun himmatu domin taimaka wa 'yan- gudun hijirar da kayayyakin abinci da magunguna da dai sauransu.

Mahukuntan sun kuma ce suna kokarin ganin an tabbatar da tsaro a yankin na Wukari domin jama'a su samu kwanciyar hankali.