Batirin da hasken rana ke caji

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fasahar za ta rage kudin samar da batirin wutar lantarkin hasken rana fiye da yadda ke tsammani

Masu bincike sun gano wata hanyar samar da batirin samar da wutar lantarki da hasken rana ke cajinsa.

Masu binciken na jami'ar Liverpool sun gano hanyar sauya sinadarin cikin batirin mai lalacewa da wani sinadarin na daban.

Masanin ya gano cewa ana iya amfani da gishirin magnesium chloride maimakon sinadarin da ake amfani da shi yanzu mai hadari ga lafiya.

Dr John Major jagoran masu binciken ya ce da alamu aikin tawagar tasa na iya kaiwa ga samar da batirin a farashi mai rahusa.

Hanyar kare lafiyar ma'aikatan da suke yin batirin yanzu na daga abin da ke haddasa tsadar batirin da ake amfani da shi yanzu.