Kira ga Putin na daukan matakan zahiri a Ukraine

John Kerry Hakkin mallakar hoto AFPGetty
Image caption Mr Kerry ya ce dole Rasha ta nuna cewa da gaske ta ke wajen tabbatar da zaman lafiya a Ukraine

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci shugaba Putin na Rasha da ya fito fili ya yi kira ga 'yan awaren da ke goyon kasar sa a Ukraine da su ajiye makamansu.

Da yake jawabi bayan wani taron ministocin harkokin wajen kungiyar kawancen tsaro ta NATO da aka yi a Brussels, Mr Kerry ya ce dole ne Rasha ta tabbatar da kalamanta na ganin an samu zaman lafiya a zahiri, ciki har da harda kokarin ganin an saki masu sanya idanun da 'yan aware suka yi garkuwa da su.

Tun farko shugaban kungiyar kawancen ta NATO, Anders Fogh Rasmussen ya bukaci Rasha da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta akan Ukraine, inda ya ce babu wani sauyi dangane da abinda ya kira haramtattun matakan da ta dauka.

Karin bayani