Ana zaben 'yan majalisa a Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'yan kasar ta Libya ba su yanke kauna ba daga wannan zaben ya haifar musu da sahihin tsarin na dimokradiyya ba.

Masu zabe a Libya na fita rumfunan zabe ranar Laraba domin zaben sabbin 'yan majalisar dokoki.

Sabuwar majalisar za ta maye gurbin wadda ake da ita yanzu wadda cece-kuce kan bambamce-bambancen akida da manufar siyasa suka dabaibaye.

Wannan dai shi ne zaben 'yan majalisa na biyu a kasar tun bayan kawo karshen yakin da ya kai ga tumbuke dadadden shugaban kasar Kanal Mu'ammar Ghaddafi daga kan mulki a shekara ta 2011.

Wata wakiliyar BBC a Tripoli ta ce wannan zaben zai gudana ciki wani yanayi da ya sha bamban sosai da wanda aka gudanar da zaben farko a cikinsa kusan shekaru biyu da suka wuce; saboda yadda rarrabuwa kai ta kara fadada tsakanin kungiyoyin mayaka masu karfin iko wadanda a baya suka jera kafada da kafada da juna a fagen daga.

Karin bayani