Microsoft ya kera wayar salularsa ta farko

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Microsoft ya kammala sayen bangaren kera wayoyin Nokia ne ranar 25 ga watan Afrilu.

Kamfanin manhajar na'ura mai kwakwalwa na Microsoft ya fitar da wayar salularsa ta farko bayan kammala sayen sashen kamfanin Nokia mai kera wayoyin na salula.

Wannan wayar da aka saka wa sunan Nokia X2 ta na amfani da manhajar Android ne.

Galibi ana daukar manhajar ta Adroid da Kamfanin Google ya kirkiro a matsayin kishiya ga manhajar wayar salula ta kamfanin na Microsoft wato Windows Phone OS.

Microsoft ya ce sabuwar wayar ta Nokia X2 ta ba shi damar da sada abokan huldarsa da wasu ayyukansa na naurar intanet, wadanda yawanci wayar ke fito wa da su a matsayin manhaja.

Karin bayani