Kotu ta dakatar da Majalisa tsige Nyako

Image caption Kotu ta dakatar da yunkurin Majalisar Adamawa kan tsige Gwamnan

Wata babbar Kotu a Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta bada umarnin cewa Majalisar dokokin Jihar da kuma kakakinta su dakatar da duk wani yunkuri na tsige gwamnan Jihar Murtala Nyako da mataimakinsa Bala Nigilari.

Sai dai Majalisar dokokin Jihar ta ce ba zata yi aiki da wannan umarni na kotu ba domin Majalisar ba a karkashin kotu take ba.

Tun a makon jiya ne dai majalisar dokokin ta zartar da kudurin bai wa gwamnan da mataimakinsa takardar shirin tsige su bisa zarge-zargen almundahana da dubban miliyoyin naira, amma kawo yanzu takardar bata shiga hannun gwamnan ba, sai dai majalisar ta wallafa ta wasu jaridun kasar bayan da ta ce ta kasa samun gwamnan gaba da gaba.

Babbar Kotun ta umarci Majalisar ta dakata da shirin tsige gwamnan da mataimakinsa sai an yanke hukunci kan karar da gwamnan da jam'iyyarsa ta APC suka shigar suna kalubalantar hanyar da Majalisar ke bi wajen tsigewar.

Wannan dai shi ne karon farko da Majalisar dokokin Jiha a Najeriya ke yunkurin tsige Gwamna da mataikinsa baki daya a lokaci guda tun bayan komawar Najeriyar ga mulkin dimokradiyya a 1999.

Masharhanta da dama da shi kansa bangaren gwamna Murtala Nyako na zargin cewa 'yan Majalisar dokokin Jihar ta Adamawa akasarin 'yan jam'iyyar PDP; na rawa da bazar fadar shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne wajen shirin tsige gwaman sabo da sabanin dake tsakanin shugaban kasar da gwamnan ta fuskar jam'iyyar siyasa da kuma batun tabarbarewar tsaron kasar, amma 'yan Majalisar na musanta zargin na cewa da ga Abuja ake ingiza su.

Karin bayani