'Yan Afrika na son Shugabanninsu su yi noma

Image caption Noma na da mahimmanci ga Shugabannin Afrika

'Yan Afrika sama da miliyan biyu sun rattaba hannu a kan wani koke da wata Kungiya ta mika wa Shugabanin kasashen Nahiyar kan su ba harkar noma muhimmanci.

Kungiyar ONE.org ta rubuta koken ne bayan da ta kaddamar da wani gangami mai suna 'kuyi noma yana biyan bukata' a watan Janairun bana.

Wannan koken dai an mikawa wasu shugabannin kasashen Afrika hannu da hannu da suka hada da na Tanzania da Benin da Ghana da kuma Senegal.

Wasu kasashen kuma an ba Ministocin da ke kula da aiyukan noma kamar na Najeriya da Burkina Faso.

Wannan gangamin na dada samun karbuwa ne a daidai lokacin da Shugannanin Afrika ke taro a Malabo da ke kasar Equatorial Guinea.

Karin bayani