Amazon na fuskantar kalubale

Image caption Amazon ya tayar da hankalin kamfanonin Birtaniya na littattafai a kan bukatar

Kamfanin samar da littattafai da sauran kayayyaki ta Intanet na Amazon na fuskantar kalubale daga kamfanonin Birtaniya na buga littattafai.

Amazon na neman a ba shi izinin buga littattafai ne idan kamfanonin suka kasa samar da wadatattu da ake bukata.

Haka kuma kamfanin yana neman a rika ba shi farashin littattafai kamar yadda kamfanonin na Birtaniya ke bai wa 'yan kasuwa.

Ya ce yana son a bashi wannan dama ce kamar sauran dillalai domin gudun samun bambanci a farashi tsakaninsu.

Wani matsakaicin kamfani daga cikin masu korafin na Birtaniya ya zargi Amazon da kokarin kashe harkar cinikin littattafai.

A kokarin tallafa wa kananan kantinan sayar da littattafai gwamnatin Faransa a ranar Alhamis, ta yi dokar hana Amazon da sauran kamfanonin sayar da littattafai ta intanet kai littafin da aka rage wa farashi ga masu saye har gida a kyauta.

Hakkin mallakar hoto AP

Kamfanin na Amazon yana da kayan buga littattafai da yawa kuma da sauri, ba kamar yadda sauran kamfanoni ke yi ba.

Sai dai kuma ana ganin wannan tsarin na samar da littattafan da dama cikin dan lokaci, ya sa littattafan ba su da inganci sosai.

A kan wannan masu buga littattafan ke ganin idan aka ba wa Amazon wannan dama, masu sayen littattafai za su zarge su da ha'inchi.