Amurka ta yi tur da harin bam a Abuja

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Amurka na nuna alhinin harin bam a Abuja

Amurka ta yi kakkausar suka game da harin bam din da aka kai Abuja, babban birnin Nigeria lamarin da ya sa mutane 21 suka mutu.

A wata sanarwa da ofishin Jakadancin Amurkan da ke Abuja ya fitar ya ce, hare-hare kan wadanda basu ji ba ba su gani ba wani mummunan laifin ne.

Sanarwar ta kara da cewa ofishin yana mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda alamarin ya shafa.

Kuma Amurka na kira ga duk 'yan Najeriya ba tare da la'akari da yanki ko addini ba, da su hadu baki daya don marawa yunkurin kawo karshen wannan laifin cin zarafin bil'adaman.

Amurka ta ce tana ci gaba da jajircewa kan taimakon mutanen Najeriya da gwamnatin Najeriyar wajen yakar ta'addanci a kasar.

Karin bayani