An saki 'yar Sudan da ta bar Musulunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bayan an sake sakin ta Meriam Ibrahim ta sheda wa BBC cewa, har yanzu ita kirista ce.

Matar nan 'yar kasar Sudan, da kotu ta saki bayan hukuncin kisa da aka yanke mata saboda ridda aka kuma kara kamata an sake ta a karo na biyu.

Meriam Ibrahim ta tafi ofishin jakadancin Amurka da ke Khartoun babban birnin kasar ta Sudan bayan sakin nata.

Mijinta dan Sudan ta Kudu ne amma kuma yanzu ya zama dan Amurka.

A ranar Litinin ne aka sake ta daga gidan yari a zaman jiran hukuncin kisa da take yi,amma kuma aka sake kamata bayan kwana daya a kan zargin ta yi takardun jabu domin barin Sudan zuwa Amurka.

Sharia'r da aka yi mata kan barin addinin musulunci ta koma kirista ta jawo suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam da wasu kasashen yammacin duniya