'Shan ruwa ana cin abinci na rage kiba'

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Mutane a yanzu na guje wa shan bakin ruwa duk da sinadaran kara lafiyar da yake da su

Kwararru sun ce kamata ya yi kananan yara su dinga shan bakin ruwa kadai a lokacin cin abinci don magance matsalar kiba.

Ayarin masana kimiyyar abinci mai gina jiki ne ya ce ruwan zaki ba shi da sinadarin calories da ake samu a cikin abinci kuma mutane sun watsar da dabi'ar shan ruwa yayin cin abinci.

Wannan kira ya zo ne lokacin da Cibiyar tabbatar da lafiyar al'ummar Ingila ke shirin wallafa matakan rage shan sukari a kasar.

An ba da shawarar cewa kamata ya yi mutum ya dinga samun sinadarin calorie fiye da kaso 11 cikin 100 daga sukarin Kamfani da zuma da lemuka da sauran ruwan zaki.

Masana abinci mai gina jiki, sun ce ba abu ne mai sauki ba tunkarar matsalar kiba fiye da kima.

Sai dai, Masanan sun fi hararar shan ruwan zaki.

Farfesa Susan Jebb ta Jami'ar Oxford ta ce gwamma a nemi wani abu daban, shawara dai ga iyaye ita ce su karfafa gwiwar 'ya'yansu su dinga shan bakin ruwa.

Ta ce ana iya ba jarirai madara bayan an yi yaye, amma dai ruwa yana da muhimmanci.

Shi ma shugaban sashen kimiyyar abinci mai gina jiki da kula da ciwon suga a King's College ta London, na cewa kamata ya yi yara su rungumi dabi'ar shan ruwa.

Matsalar ita ce mutane a yanzu kwata-kwata ba su damu da shan ruwa ba. Ina ganin ya kamata iyaye su dinga nuna wa 'ya'yansu ruwa amma ba abin shaye-shaye na kwadayi ba.

Ayarin kwararrun ya ce babban tasirin sukari ga lafiya shi ne ya kasance wata kafar sinadaran calories da za su taimaka wajen rage kiba, sai dai shaidun da ake samu yanzu na nuna cewa babban kason sinadaran da ake samu daga sukarin yana iya yin lahani.

Suka ce sukari ka iya kara barazanar cutukan zuciya da cutar suga rukuni na 2, baya ga taibar da yakan janyo.

Tuni dai Hukumar lafiya ta duniya ta fitar da jadawalin tsare-tsare da ke jaddada cewa bai kamata yawan sukari ya zarce kaso 10 cikin 100 na sinadaran da mutum ke sha a kullum ba, kamata ya yi ma mutane su tsaya a kaso 5 cikin 100.