Mutane10 sun mutu a wata fashewa a Bauchi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba ma an kai harin bam rukunin shagunan Emab Plaza da ke Abuja inda mutane sama da 20 suka mutu

Wani abu da ake kyautata zaton bam ne da ya fashe a wani gidan karuwai a birnin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya hallaka mutane 10 da jikkata wasu 14

Lamarin ya faru ne a unguwar Bayan-Gari da ke cikin birnin na Bauchi, da kusan karfe goma na daren Juma'a, yayin da jama'a ke holewa a unguwar wadda ta yi suna da wuraren rawa da mashaya.

Kakakin rundunar yansandan jihar ta Bauchi, DSP Haruna Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da ko hari ne na kunar bakin wake ko kuma dasa abin fashewar aka yi ba.

Karin bayani