Facebook na kalubantar umarnin kotu

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Facebook ya ce an hana shi bayyana shari'ar sai a wannan makon

Facebook na kalubalantar umarnin wata kotun Amurka, da ta tilasta masa ya bayar da bayanan mutane kusan 400 da ke cikin shari'ar zamba.

Kamfanin na dandalin sada zumunta, ya ce, bukatar ita ce mafi girma da ya taba samu daga wata hukuma ta gwamnati.

A shekarar da ta gabata ne aka mika wa kotun wadda ke New York hotuna da sakonnin rubutu na waya da sauran bayanai na mutanen.

Amma kuma sai a cikin wanan makon ne wani alkalin kotun ya bayyana matakin karbar.

Shari'ar ta danganci binciken zamba ce da mutanen ake zargin sun yi, ta karbar kudaden tallafin nakasassu, alhalin lafiyarsu kalau kamar yadda shafinsu na Facebook ya nuna.

Hakkin mallakar hoto AFP

A kan hakan ne kotun ta umarci kamfanin shafin na Facebook da ya bayar da bayanan shafuka 381 wadanda kotun ta ce sun dauke da shedun miyagun laifuka.

Bayan hana Facebook din damar daukaka kara, sai ya bi umarnin, amma kuma da korafin cewa, ya saba wa kundin tsarin mulkin Amurka na ba da kariya ga bincike da karbe wani abu ba bisa ka'ida ba.

A farkon shari'ar kotun ba ta bayyana ta ga jama'a ba, amma bayan da Facebook ya daukaka kara, sai alkalin kotun ta New York ya bayyana shari'ar.

Facebook ya kuma ce gwamnati ta nemi abin da ya kira wasu dokoki na daban, da suka hana shi gaya wa masu amfani da shafin cewa an tilasta ma sa ne ya bayar da bayanan a kansu.

Daga cikin mutane 381 da ake binciken a kansu, an tuhumi 62 a shari'ar ta zamba.