'Abin da ya sa ba na maganar 'yan Chibok'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jonathan na kokarin wanke kansa

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya rubuta wasika ga jaridar 'The Washington Post' ta Amurka inda ya bayyana dalilan da suka sa ya yi shiru game da 'yan matan Chibok da aka sace.

Fiye da watanni biyu kenan da 'yan Boko Haram suka sace daliban su fiye da 200 a makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.

Mr Jonathan ya ce shirunsa ya zama dole saboda baya son ya kawo tsaiko a wajen binciken da ake gudanarwa game da lamarin.

A cewarsa, ya damu matuka saboda masu sukarsa na amfani da shirun da ya yi suna nuna kamar ya gaza ne.

'Yan Nigeria na caccakar Mr Jonathan a kan cewar gwamnatinsa ta kasa shawo kan matsalar Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram ta hallaka dubban mutane a Nigeria tun daga shekara ta 2009.

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Masu zanga-zanga kan 'yan matan Chibok
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi taro a Paris da London kan batun Boko Haram

Karin bayani