Ramadan: Fasto ya fito da fursunoni Musulmi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana samun tashe-tashen hankula mai nasaba da addini da kuma kabilanci a Kaduna

Yayin da watan Azumin Ramadan ke daf da kamawa, shugabannin addinai na kara tashi tsaye domin ganin an kara samun kwanciyar hankali da hadin kai.

A jihar Kaduna da ke Najeriya wani limamin kirista ya fito da wasu fursunoni Musulmi wadanda aka kulle saboda ko dai sun kasa biyan tarar da aka yi masu, ko kuma sun aikata karamin laifi.

Faston ya ce ya fitar da fursunonin ne saboda su je su yi azumin Ramadan tare da iyalansu, ganin girman watan.

Fursunonin da aka fito da su dai sun nuna farin ciki saboda fitar da su daga halin da suka bayyana da na kunci.