'Da wuya Nigeria ta magance Boko Haram'

Jami'an tsaro a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

A Najeriya, mahalarta babban taron kasar sun ce matukar mahukunta ba su inganta rayuwar jami'an tsaro ba, da wuya a iya magance Boko haram.

Mahalarta taron sun yi zaman sirri ne lokacin da kwamitinsu na tsaro ya gabatar da rahoto da kuma shawarwarinsa.

A cikin rahoton nasa kwamitin ya ayyana matsaloli da dama da ya ce suna addabar jami'an tsaro da kuma ayyukansu.

Ciki kuwa in ji rahoton har da rashin iya tattara bayanai da sarrafa su tsakanin junansu, da rashin kayan aikin da za su iya fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram.

Batun bai wa jihohin damar kafa rundunar 'yan sanda a matakin jihohi dai abu ne da ya ja hankali da zazzafar mahawara a taron kasar.