Ukraine ta bude sabon babi - Poroshenko

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Poroshenko ya ce an bude sabon babi a tarihin Ukraine

Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko, ya bayyana rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kara alaka da tarayyar Turai da cewa sabon babi ne a tarihin kasarsa.

Sai dai ya ce kasar ta Ukraine ta tafka babbar hasara ta fuskar tattalin arziki, sakamakon yadda mutumin da ya gada, Viktor Yanukovych, ya ki amincewa da shirin, ya goyi bayan karfafa alaka da Rasha maimakon haka, lamarin da ya janyo tarzomar da ta yi sanadiyar kifar da shi.

Shugaba Poreshenkon ya ce yana duba yuwuwar kara wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta kashin kai dake aiki yanzu da tsawon kwanaki uku a gabashin kasar ta Ukraine.

Daga ranar Juma'a ya kamata ta kare, koda yake ana ci gaba da fada a wasu sassa na yankin.

Shugaba Putin dai yayi kiran da a yi shelar tsagaita wuta ta lokaci mai tsawo, domin ta bada damar yin tattaunawa tsakanin gwamnatin Ukraine da yan aware masu goyon bayan Rasha dake gabashin kasar.

Karin bayani