Ebola: WHO ta gargadi Afrika ta Yamma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption WHO, ta ce wayar wa da mutane kai kan hadarin cutar, shi ya fi maimakon takaita tafiye-tafiye a yaki da ita

Hukumar lafiya ta duniya , WHO, ta yi kira ga kasashen yankin Afrika ta yamma da cutar nan ta Ebola mai kisa ba ta bulla ba, da su shirya wa zuwanta.

Kusan mutane 400 ne dai cutar ta hallaka a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo tun lokacin da ta barke a farkon shekaran nan.

Hukumar lafiyar ta duniya ta na gargadin cewa yadda iyakokin kasashen yankin suke wasarere, hakan ya sa cutar za ta iya bazuwa cikin sauki a tsakaninsu.

Wani likita a Sierra Leone Dr Shek Moar Khan, ya ce kalubalen da suke gamuwa da shi kan yaki da cutar, shi ne yadda mutane suka dauka cewa cutar wani abu ne da ya danganci iskoki kawai.