BT ya nemi afuwar rashin Intanet

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption BT na gudanar da binciken matsalar Intanet

Kamfanin samar da Intanet na BT ya nemi afuwa bayan da masu amfani da Kamfanin da dama a Birtaniya suka kasa shiga Intanet.

Sai dai yanzu kamfanin ya ce an warware wannan batu

Masu amfani da Kamfanin sun ce sun kasa kama wasu shafukan Intanet da suka hada da na sada zumunta da bankuna da shafukan sayayya saboda matsalar

BT ya ce ba zai iya cewa ga yawan kostomomin da wannan matsala ta shafa ba

Amma an bada rahotan wannan matsala a yankuna da dama a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mai magana da yawun kamfanin BT ya ce ‘muna bada hakuri game da duk wani cikas da wannan matsala ta haifar’.

Kamfanin wanda yake da kostomomi kimanin miliyan bakwai a Birtaniya ya ce har yanzu yana binciken lamarin.

Wani sako da BTCare ya rubuta a shafin Twitter na cewa: Muna bada hakuri game da matsalar da mafiyawancin ku suka gamu da ita wajen kama Intanet’.

‘A yanzu an warware matsalar, muna bada hakuri game da duk wani cikas da aka samu’