Sarki Abdullah: 'Yan ta'adda na fakewa da addini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saudiyya tace ba zata bari 'yan ta'adda su sa kasar a gaba ba.

Sarki Abdullah na Saudi Arabia, ya yi suka kan abin da ya kira, fakewar da 'yan ta'adda ke yi da addini suna tafka ta'asa.

Sarkin ya yi sukar ne a jawabin da ya gabatar na fara azumin watan Ramadhan.

Sarki Abdullah ya jaddada cewa, musulunci addini ne na hadin kai, da hakuri, yana mai bayar da tabbacin cewa ba zai taba bari 'yan ta'adda su sa kasarsa a gaba ba.

Masu aikewa da labarai sun ce Saudi Arabian, na wadannan kalamai ne, sakamakon mamayar da 'yan gwagwarmayar Islama na kungiyar ISIS ke yi a makwabciyarta Iraq.