Ana bukukuwan fara yakin duniya na daya

Hakkin mallakar hoto AFP

Ana gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 100 a nahiyar Turai, tun bayan da wani matashi dan kabilar Sabiya, mai ra'ayin kishin kasa, ya hallaka mai jiran gadon sarautar daular Austria da Hungary.

Lamarin ne ya haddasa wasu lamurran da suka janyo yakin duniya na daya.

Jama'a a birnin Sarajevo sun taru domin tunawa da ainihin lokacin da Gavrilo Princip, ya bindige Archduke Franz Ferdinand tare da matarsa, bayan sun yi batan kai sun bi wata hanya, a cikin motarsu marar rufi.

Anita Hoenberg, wata tattabakunnen wanda aka kashen, ta gaya wa BBC cewa, "kakan- kakan nata ba zai so a yi yaki ba."

An fara bukuwan ne tun ranar Alhamis da wani taron shugabannin kasashen Turai asihirin da shidda a birnin Belgium.

Ana saran kammala bukukuwan ne da wasu kade-kade da raye-raye a wani gidan adana littafai a da aka sake ginawa bayan an lalata shi a yakin Bosnia na shekarar 1992