An kashe mutane 46 a kusa da Chibok

Makarantar da aka sace 'yan mata fiye da 200 a Chibok Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A garin Chibok ne aka sace dalibai fiye da 200 daga makarantar sakandaren 'yan mata

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan wadansu garuruwa hudu a kusa da Chibok dake jihar Borno a Najeriya.

Rohotannin sun ce harin ya yi ajalin sama da mutane 40.

Wani dan banga a daya daga cikin garuruwan da abun ya shafa, ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa an kai harin ne a kan garuruwan Kautikari, da Nasarawa, da Gwaradina, da kuma Kwadake, inda aka hallaka "mutane 46."

Ya kara da cewa 37 daga cikin su mazauna kauyukan ne; mutane 3 kuma 'yan banga ne; yayinda kuma 6, maharan ne.

Sai dai kuma ya ce, ba mamaki adadin wadanda suka mutum ya karu domin har ya yanzu ba'a san inda wasu mutane da dama suka ba.

A gobe ne a cewar sa ake sa ran yin jana'izar mamatan.

Rohotanni sun ce har yanzu ana zaman dar-dar a kauyukan da abun ya shafa.

Kawo yanzu dai hukumomi basu ce komi ba akan hare-haren.

Dazu da safe ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a kauyukan lokacinda jama'a ke ibada a coci-coci.

A watan Afrilun da ya wuce ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata sama da 200 daga garin na Chibok, kuma har yanzu ba a gano su ba.

Karin bayani