ISIS ta yi ikirarin kafa daular Islama

Abu Bakr al-Baghdadi, shugaban kungiyar ISIS Hakkin mallakar hoto

Kungiyar masu gwagwarmayar Musulunci na ISIS tace zata kafa daular Musulunci.

Wani kakakin kungiyar ya bada sanarwar cewa, za su hade yankunan da ke karkashin ikonsu a Iraki da Syria, domin kafa daular Musulunci.

A cewar kakakin, yankin zai kama daga Aleppo, a arewacin Syria, ya dangana da Diyala, a gabashin Iraki.

Saboda da haka, in ji mai magana da yawun ISIS din, a yanzu kungiyar ta takaita sunanta daga 'Kasar Musulunci a Iraki da Syria' zuwa 'Kasar Musulunci' kawai.

Kungiyar ISIS din ta ce ta nada jagoranta - Abu Bakr al-Baghdadi - a matsayin Kalifa, wanda ta ce shine jagoran dukan Musulmi.

Karin bayani