An "kashe mutane 25" a Kaduna

Hakkin mallakar hoto KDGH
Image caption Tun a makon da ya gabata ake samun tashe tashen hankula a yankin kudancin Kaduna

Rohotanni daga jihar Kaduna a arewacin Najeria sun ce kimanin mutane ashirin da biyar aka hallaka a karamar hukumar Sanga.

Wasu 'yan bindiga ne da ba'a tantance ko su wanene ba suka kai ma garin hari.

Shugaban karamar hukumar ta Sanga, Mista Emmanuel Dan Zaria ya shaidawa BBC cewa maharan sun "kashe mutum ashirin-da-biyu a kauyen Ambe."

Ya kuma kara da cewa maharan sun kashe karin wasu mutanen ukku a wani kauyen.

Sai dai kuma kwamishinan 'yan sandan jihar, ya ce mutane ukku ne suka mutu a harin.

Tun a makon da ya gabata ne dai ake samun tashe tashen hankula a yankin, bayan harin da aka kai a garin Fadan Karshi, a karamar hukumar ta Sanga.

An jima ana samun tashin hankali a jihar da ma wasu jihohin arewacin kasar tsakanin makiyaya da manona.