Gwajin na'urar sauka a duniyar Mars

Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Na'urorin daukar hoto sun nadi yadda aka cilla na'urara zuwa duniyar ta Mars.

Hukumar kula da harba kumbu zuwa sararin samaniya a Amurka ta yi nasara a gwajin da tayi na wata sabuwar fasahar harba mutane zuwa duniyar Mars.

An harba wata naura mai kama da tukunyar tasa ne tare da wata sabuwar rigar iska da kuma wani zobe da ake cika wa da iska zuwa sararin sama domin a gani ko za su iya taimaka wa wajen rage wa kumbu gudu sa'adda ya kusanci doron duniyar ta Mars.

Dukkan na'urorin uku sun yi aiki yadda ake so in ban da rigar iskar wadda ta ki budewa sosai.

An dai harba na'urarorin ne daga tsibirin Hawaii.

Hukumar ta NASA na fatan darussan da aka koya daga wannan aikin, za su ba ta damar kai na'urorin hakar ramukka masu nauyi a duniyar ta Mars.

A halin da ake ciki yanzu iyakar nauyin da za a iya kai wa zuwa duniyarta Mars shin ne nauyin ton daya da rabi.

An dai riga an baza masu bincike zuwa sassa daban-daban na duniya domin gano inda na'aurar nadar bayanan ta fada.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yadda 'yan sama jannati ke sauka kan duniyar ta Mars kafin wannan na'urar.