Ghana na fuskantar karancin man fetur

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ghana na danyen hako man fetur, amma kuma tana shigo wa da tatacce

Ana samun dogwayen layuka a gidajen sayar da man fetur a Ghana, lamarin da ya jefa mutane cikin wani hali.

Hakan ya biyo bayan daina samar da man da kamfanonin da ke shigo da man suka yi, saboda suna bin gwamnati bashin fiye da kudi sabon Cedi miliyan Dubu daya.

Lamarin da ya sa babu man fetur a gidajen mai da dama na kasar.

Sai dai gwamnatin kasar ta ce tana da man da ta adana, wanda ta fara sayar wa ga jama'a domin rage radadin halin da ake ciki.