Tsaro: 'Yan sanda sun gana da Hausawa a Lagos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana zargin 'yan kungiyar Boko Haram sun shiga Lagos

Rundunar tsaro ta 'yan sandan Najeriya a jihar Lagos ta gana da wasu shugabannin al'ummar Hausawa mazauna jihar.

An gudanar da ganawar ne a wani yunkuri na inganta harkokin tsaro da kuma yiwuwar kaucewa tashin tarzoma a tsakanin al'ummomin jihar ta Lagos.

Hakan dai yazo a sakamakon yadda ake rade-radin shigowar wasu da ake zargin 'yan kungiyar nan ce ta Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Waljihad da aka fi sa ni da suna Boko Haram cikin birnin na Lagos.

Wasu shugabannin Hausawa mazauna Lagos dai sun bukaci rundunar 'yan sandan da ta yi irin wannan ganawa tare da sauran al'ummomin Jahar.