Oscar ba shi da tabin hankali - Likitoci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A bara ne Oscar ya harbe Reeva a bandakin da ke gidansa

Likitocin da ke kula da masu tabin hankali sun shaida wa kotu cewa zakaran dan wasan tseren nan na Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius ba shi da tabin hankali.

Kotun ta koma zama ne a ranar Litinin bayan shafe makonni shida tana hutu, domin bai wa likitocin damar tantace ko Mr. Pistorius na da tabin hankali.

Lauya mai kare wanda ake kara dai ya ce Oscar na fama da tabin hankali a lokacin da ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Za a ci gaba da sauraron karar nan da makonni biyu masu zuwa a kotun da ke zamanta a Pretoria a Afrika ta Kudu .

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba