An halaka mai daukar hoton Rasha a Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A yau za'a kawo karshen tsagaita wutar da aka cimma

Wani gidan Talabijin mallakar gwamnatin Rasha ya ce an kashe daya daga cikin masu yi masa daukar hoto a gabashin Ukraine.

Gidan Talabijin na Channel One Russia ya ce Anatoly Klyan ya mutu ne kusa da wani sansanin soji a Donetsk.

Shugabannin Ukraine da Rasha da Jamus da Faransa zasu gudanar da karin tattaunawa a yau Litinin dangane da yadda za'a warware rikicin gabashin Kasar

Jamus da Faransa sun bukaci Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya fadada tsagaita wutar da aka cimma a karo na biyu.

Ana saran yau za a kawo karshen tsagaita wutar

Amma daruruwan masu zanga zanga sun hallara a Kiev a ranar Lahadi domin kira da a dawo da farmakin soji akan 'yan bindigar masu goyan bayan Rasha