'Mun kama dan leken asirin Boko Haram'

Alex Badeh Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babu dai wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin.

Rundunar Sojan Najeriya ta ce jami'anta sun fasa wani gungun 'yan leken asiri na 'yan Boko Haram tare da kama wani dan kasuwa da tace yana da hannu dumu-dumu a sace 'yan matan nan 'yan makaranta su fiye da 200.

Ma'aikatar tsaron Najeriyar ta ce dan kasuwar Babuji Ya'ari na da'awar dan banga ne da ke taimakawa wajen yakar Boko Haram, amma kuma dan ta'adda ne.

A cikin wata sanarwa, kakakin ma'aikatar tsaro Manjo-Janar Chris Olukolade ya ce Babuji Ya'ari ne ya jagoranci kisan-gillar da aka yi wa sarkin Gwoza a watan Mayu; kuma shi ne ya tsara wasu hare-hare da suka hallaka daruruwan mutane a Maiduguri tun daga shekara ta 2011.

Ya ce bayanin da suka samu bayan kama Mr. Ya'ari ne ya taimaka musu wajen kama wasu mata biyu da suka hada da Hajiya Kaka wadda ya ce 'yan leken asiri ce ga kungiyar wadda ke kuma sayo wa 'yan ta'adda makamai, da kuma Hafsat Bako, wadda ita ce ke biyan maharan kungiyar ta Boko Haram bayan sun kai hari.

Karin bayani