Bam ya hallaka mutane 18 a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Mutane akalla 18 ne suka rasu sannan wasu fiye da 55 sun samu raunuka sakamakon fashewar bam a wata kasuwa a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.

Wani jami'in asibiti a Maiduguri ya shaidawa BBC cewar yanzu haka ana baiwa mutanen da suka jikkata kulawa.

Bayanai sun nuna cewar an dasa bam din ne a cikin wata mota kirar 'pick up', mai dauke da gawayi a kasuwar da ake kira 'Monday Market'.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin amma dai, jihar Borno ta kasance cibiyar kungiyar Boko Haram.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewar rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da 650,000 da muhallinsu.

Kusan watanni uku kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai kusan 300 a Chibok kuma kawo yanzu babu bayanai game da inda 'yan matan suke.

Sai dai kuma ma'aikatar tsaron Nigeria ta yi ikirarin kama wani babban dan leken asiri na Boko Haram mai suna Babuji Ya'ari wanda ta ce yana da hannu wajen sace dalibai a Chibok.

Hakkin mallakar hoto Isa Gusau
Image caption Gwamna Kashim Shettima ya ziyarci wadanda suka samu raunuka
Hakkin mallakar hoto Isa Gusau

Karin bayani