An kara farashin fetur da iskar gas a Kamaru

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamaru na da arzikin man fetur

Gwamnatin Kamaru ta kara farshin man fetur da na iskar gas lamarin da ake fargabar zai janyo hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Karin farashin litan mai fetur da dangoginsa da hukumomin kasar suka yi ya fara aiki ne a ranar Talata .

Sai dai kuma gwamnatin ta ce za ta fara tattauna batun Karin albashi.

Amma kuma nan take ta rage kudin da jama'a ke biya na wasu haraji.