Taron gaggawa kan cutar Ebola a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sa ran jami'an lafiyar su tsara yadda yankin zai tunkari cutar ta Ebola.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kira wani taron gaggawa a Ghana, domin tattauna cutar Ebola da ministocin 11 na yammacin Afrika.

Taron na kwanaki biyu zai tattauna hanyoyin dakile kwayar cutar ta Ebola daga yaduwa zuwa sauran sassan Afrika ta Yamma.

Taron dai na zuwa ne bayan kiran da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi ga kasashen na su hada gwiwa domin dakile bazuwar cutar ta kan iyakokinsu.

Cutar da ta fara bulla a Guinea ta bazu zuwa Liberia da Kuma Saliyo, kuma tuni cutar ta hallaka mutane kusan 400 a yankin.

Karin bayani