Kotu ta amince da haramta sa nikabi a Faransa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasar Belgium ma ta kafar irin wannan dokar

Wata kotun kare hakkin bil'adama ta Tarayyar Turai ta amince da haramcin sanya nikabi a bainar jama'a a Faransa.

Wata mata 'yar Faransa mai shekaru 24 ce ta shigar da karar tana mai cewa haramcin ya keta 'yancinta na yin addini.

Sai dai kotun ta yanke hukuncin cewa hukumomin Faransa suna da kwararan hujjoji na tabbatar da zaman lumana a tsakanin al'umma.

Shekaru hudu da suka wuce ne kasar ta Faransa ta kafa dokar haramta sanya nikabin.