Google zai gurfana a kotu kan leken sirri

Hakkin mallakar hoto
Image caption Google dai kamfani ne mallakar kasashe da dama da ke da mazauni a Amurka

Kotun koli a Amurka ta yi watsi da daukaka karar da shafin matambayi-ba-ya-bata na Google ya yi na neman ta yi watsi da kararrakin da aka shigar kansa kan karya dokokin hana leken sirrin wani.

A shekara ta 2010 Google ya amsa cewa ya debo wasu bayanai daga wasu shafukan sirri na wasu a bisa kuskure, sa'adda ya ke shirya manhajarsa ta jagoran hanyoyi.

Wasu na'urorinsa sun bude shafukan E-mail, da sunayen shiga shafi da da kuma kalmomin sirri na bude shafi ba da iznin masu su ba tsakanin shekara ta 2008 da ta 2010.

A cewar jaridar USA Today, Google na fuskantar kararraki kusan goma sha biyu, kuma wadanda ke karar kamfanin suna kara matsa kaimi yanzu.

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Yadda manhajar jagoran hanyoyi ta google ta ke.

Ta ce a shekarar 2011 an dunkule kararrakin zuwa kara daya a wata kotun tarayya da ke San Francisco.

Ana zargin Google da karya wata dokar Amurka da ake kira ''Wiretap Act'' wadda ke kayyade yadda ake debo bayanai daga shafukan intanet ta kuma haramta dibar bayanan ba tare da izni ba.

BBC ta gano cewa Google na ja cewar bayanin da ya diba ya fada karkashin wani sashe na dokar ne wanda ya ba da damar dibar bayanai ta naura mai kwakwalwa idan kowa zai iya kai ga wannan bayani idan ya so.

A wani shafi nasa, kamfanin ya ce ''Muna son mu goge wannan bayanin ba da wani bata lokaci ba, kuma a halin yanzu muna kan tuntubar hukumomi a kasashen da abin ya shafa kan yadda za mu goge shi da sauri''

Google ya riga ya amince zai biya Fam miliyan 7 domin a kashe maganar wadda ta shafi jihohin Amurka 36 da kuma Gundumar Columbia.

Karin bayani