ISIS ta nemi mubaya'a daga 'yan tawaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption ISIS ce keda iko a wasu yankuna a Iraqi

Rahotanni daga arewacin Iraqi na cewa mayakan Sunni wadanda suka ayyana kafa daular musulunci a wani bangare na kasar, da kuma a cikin makwabciyar Kasar Syria, sun fadawa sauran kungiyoyin 'yan tawaye da su kwance damara sannan su yi mubaya'a gare su

Majiyoyin kabilu dana sojoji sunce an shaida wa sauran kungiyoyin 'yan tawayen a wata ganawa da aka yi ta kwanaki biyu a birnin Mosul na Iraqin cewa mayakan kungiyar ISIS ne kadai suke da damar daukar makamai

Wani wakilin BBC a arewacin Iraqi ya ce kungiyar tana kara karfafa kafafunta a yankunan Sunni inda ta kwace a 'yan makonnin nan.