Isra'ila ta kai hare-hare a Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-haren dai sun zo ne bayan kashe wasu samaru uku 'yan Isra'ila a kusa da Hebron.

Isra'ila ta kaddamar da wasu hare hare ta sama fiye da sau 30 a kan cibiyoyin soji na Hamas da Islamic Jihad a Gaza.

Ma'aikatar cikin gida ta Falasdinawa ta ce an kai hare-haren ne da nufin wargaza sansanonin Hamas wadda ke da iko da yankin na zirin Gaza da kuma na kungiyar Islamic Jihad.

Sojin Kasar Isra'ila sun ce an kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren makaman roka da mayakan Hamas suka kai akan kudancin Israila .

Sai dai Wani wakilin BBC a Gaza yace kungiyar Hamas din ta musanta kaddamar da hare haren rokar

Karin bayani