Ana bincikar otel kan sanar da bayanan abokan hulda

Image caption A ranat Talata shafin ya nuna wani sako da ke cewa ''mun rufe domin yin gyara.''

Hukumar da ke sa ido don tabbatar da boye asirin abokan hulda a shafin intanet a Burtaniya na bincikar wani shafin intanet na wani otel bisa zargin nuna bayanan wasu abokan huldarsa.

Shafin na Hotelhippo.com, mallakar otal din Hotelstay Uk ya nuna wasu bayanan abokan huldarsa da suka sayi tikitinsa.

Bayanan da aka nuna za su iya kai ga a san addirshin masu hulda da shi.

Sai dai jim kadan bayan da BBC ta tuntunbi shafin na hotelhippo.com sai aka rufe shi.

A cikin wata sanarwa Hotel din ya ce ''muna tabbatar da cewa mun rufe shafin Hotel.hippo.com domin daukar wani matakin gaggawa na shawo kan wata matsala''

''Boye bayanan abokan huldarmu abu ne mai matukar muhimmanci a gare mu, kuma mun dukufa wajen tabbatar da tsare bayanan,'' inji sanarwar.

Wani kwararre kan kare bayanai Scott Helme ya ce ya aike da bayani kan bayyanar bayanan ga hukumar Otel din ranar 25 ga watan yuni, amma bai dauki wani mataki ba sai ranar Talata.

Mr. Helme wanda ya bayyana budewar da bayanan suka yi a zaman mai bata rai, ya shaida wa BBC cewa Kamfanin na HotelStayUk ya yi biris da sakonnin e-mail da kuma kiraye-kirayen wayar da aka yi musu.

Sai dai manajan daraktan kamfanin Chris Orrell ya ce bai da masaniya dangane da batun.

Hukumar da ke sa ido don tabbatar da boye asirin abokan hulda a shafin intanet a Burtaniya za ta yi bincike kan lamarin domin gano gaskiyar lamarin.

Karin bayani