Umaru Dikko ya rasu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Margayi Umaru Dikko

Tsohon ministan sufuri a Jamhuriya ta biyu a Nigeria, Malam Umaru Dikko ya rasu sakamakon jinya a wani asibiti a London.

Malam Umaru Dikko ya rasu yana da shekaru 78 a duniya kuma tsohon ma'aikacin sashin Hausa na BBC ne.

An haifeshi a jihar Kaduna a shekarar 1936 kuma ya rike mukamai da dama a gwamnatin jihar da ta tarraya.

Margayin, shahararren dan siyasa ne a arewacin Nigeria musamman lokacin mulkin tsohon shugaban kasar, Alhaji Shehu Shagari.

Bayan juyin mulkin soji a shekarar 1984, Umaru Dikko ya fice daga Nigeria ya koma London inda ya nemi mafakar siyasa kafin ya sake dawo wa cikin kasar.