Sabon rikicin addinni a kasar Burma

Image caption 'Yan sanda sun yi kokarin kwantar da kurar rikicin

Rikici ya barke tsakanin mabiya addinnin Bhudda da kuma Musulmi a birnin Mandalay wanda shi ne birni na biyu mafi girma a kasar Burma.

Ana dai yawaita samun irin wannan tashin hankali tsakanin 'yan Bhudda da kuma tsirarun al'ummomin musulmi a shekaru ukun da suka gabata a Burma.

A tashin hankalin da aka yi cikin dare, 'yan sanda sun yi kokarin kutsa kai domin raba rikicin, amma sai dai an lalata wasu shaguna da kuma masallatai na Musulmi.

Rahotanni sun ce an tsare mabiya addinnin Bhudda su uku.

A shekarar 2012 ma, akalla mutane 200 aka kashe a wani mummunan tashin hankali tsakanin 'yan Bhudda da kuma Musulmi a jihar Rakhine.