Iraki: Saudiyya ta tura sojoji zuwa iyakarta

Hakkin mallakar hoto Getty

Rahotanni sun ce Saudiyya ta girke sojojinta dubu 30 a yankin kan iyakarta da Iraki, bayan da sojojin Irakin suka janye daga yankin.

Sai dai jami'an sojan Irakin sun musanta rahotannin, suna masu cewa har yanzu akwai sojoji da dama a yankin.

A cewar hukumomin tsaro a Irakin, akwai bataliya biyu ta soji har biyu a kan iyakar.

Tashar talabijin ta gwamnati watau Al Arabiya ta ce tuni aka tura dakarun Saudiyya zuwa kan iyakar mai tsawon gaske.

Masu aiko da rahotanni dai sun ce dangantaka ta yi tsami tsakanin Saudiyya da gwamnatin Iraki wadda 'yan Shia ke jagoranta inda wasu 'yan siyasar Irakin ke zargin Saudiyya da taimaka wa masu tada kayar baya 'Yan Sunni.