Sarkozy: ana min bita da kullin siyasa

Nicolas Sarkozy, tsohon Shugaban Faransa Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Nicolas Sarkozy, tsohon Shugaban Faransa

Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, wanda a yanzu haka ake bincikarsa bisa zargin cin hanci da rashawa, ya musanta cewa ya taka doka.

Ya ce bita da kullin siyasa ne ake yi masa.

A cikin hirar da yayi da manema labaran Faransar, Mr Sarkozy ya ce ana amfani da wani bangare na shari'a don cimma burin siyasa.

Ya ce bai taba yin wani abun da ya saba wa akidojin jamhuriyar Faransar ba.

Wakilin BBC a birnin Paris ya ce, zargin da tsohon shugaba Sarkozy yake yi karara shine cewa, masu ra'ayin gurguzu a bangaren shari'ar kasar, suna kokarin ganin bayansa don su hana shi komawa fagen siyasa.

Tun farko dai Praministan Faransar, Manuel Valls, ya dage a kan cewa gwamnati ba za ta tsoma baki a binciken da ake yi wa Mr Sarkozy ba.

Ya ce bincike ne mai zaman kansa.