Kotun Indiya ta nemi kawo shaida kan sadaki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A indiya mata ke biyan sadaki ba maza ba

Kotun kolin Indiya ta ce ana samun mata da dama da ke wuce makadi da rawa game da dokar haramta biyan sadaki.

Matan a cewar kotun suna yin hakan ne domin cin zarafin mazajensu da kuma surukansu.

Idan mace a kasar ta yi korafin cewa mijinta ko wani danginsa ya nemi ta biya sadaki, za a iya kama shi nan take, sai dai mafi yawa daga mazan ana gano cewa basu da laifi.

A yanzu kotun kolin ta bai wa 'yan sanda umarnin su tattara hujjoji da zasu gabatar a gaban alkali, kafin su kama wani bisa korafi game da sadaki.

Fiye da shekaru 50 kenan da Indiya ta haramta biyan sadaki, sai dai al'adar na ci gaba kuma masu fafutuka na cewa hakan na janyo cin zarafi ga mata wasu lokutan ta kan kai ga kisa.