Sudan ta Kudu za ta fuskanci karancin abinci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban mutanene suka mutu sakamakon tashin hankalin da ya barke tsakanin shugaba Salva Kiir da Riek Machar

Kungiyoyin agajin da ke aiki a Sudan ta Kudu sun yi gargadin cewa kimanin mutane miliyan hudu za su fuskanci karancin abinci a watan gobe.

Rikicin kabilancin da ake fama da shi a kasar ya sa mutane da dama sun gudu daga gidajensu tun a watan disambar bara.

Lamarin da yasa ba su yi noma ba ko kuma sun girbe abin da suka noma.

Kwamitin agaji na Burtaniya, Disasters Emergency Committee ta ce dan abincin da ya rage wa mutane zai kare ne a watan Agusta.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba