Amurka ta tsaurara bincike a filayen jirage

Hakkin mallakar hoto
Image caption Amurka na fargabar za a iya kai ma ta hari

Amurka ta kara tsaurara matakan tsaro tare da bincike a filayen jiragen sama dake wajen kasar, tare da jiragen da suke sauka kai tsaye cikin kasar.

Ma'aikatar tsaron cikin gida dai bata bada cikakkun bayanai ba, game da sabbin matakan da za a dauka , amma tace hakan wani bangare ne na aikin da ake na tabbatar da tsaro.

Kodayake dai ba'a bayyana cewa ana fuskantar wata barazana ba, amma wakilin BBC a Washington yace jami'ai sun damu da cewa kungiyoyin dake da tsatsauran ra'ayi a Syria da kuma Yemen maiyiwuwa na aiki tare domin kirkirar wani sabon abu mai fashewa, da ka iya kaucewa duk irin matakan tsaron da aka samar.

Ana ganin rikicin Syria yaja hankalin dubban mayakan kasashen yammacin duniya, kuma jami'ai suna fargabar cewa za'a iya amfani da daya daga cikinsu wajen tada bom.