Paparoma ya amince da fitar da aljanu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'adar fitar wa da jama'a aljanu ta faro tun lokacin samuwar addinin kirista

Fadar Vatican, ta Paparoma, ta amince a hukumance, da wata kungiya ta malaman darikar katolika su 250, da suke ikirarin ceto mutane daga shedanun aljannu.

Sabuwar kungiyar ta kunshi malaman na kiristocin masu fitar wa mutane aljannu wato, rukuyya daga kasashe 30.

Akai-akai Paparoma dai yakan yi magana a kan, shedan, kuma a bara ne ma aka dauki hotonsa yana dora hannusa kan wani yaro, da ke kan keken guragu, wanda ya bingire bayan da Paparoman ya taba shi.

Masu rukuyya dai sun ce Paparoman ya yi nufin raba yaron ne da shedan.

Fadar Vatican na dari-darin amincewa da masu ikirarin fitar da aljannu kafin yanzu.