Chibok: Za mu kai karar gwamnatin Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwanaki 81 'yan matan na hannun 'yan Boko Haram

Al'ummar Chibok mazauna Abuja ta yi barazanar kai gwamnatin Nigeria kara gaban Majalisar Dinkin Duniya idan har ta kasa kubutar da 'ya'yansu da 'yan Boko Haram suka sace.

Kwanaki 81 kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai kusan 300 a makarantar su da ke Chibok a jihar Borno, kuma kawo yanzu babu alamun gwamnati na yinkurin ceto su.

Shugaban 'yan Chibok da ke Abuja, Dr Bitrus Pogu wanda ya bayyana matsayin al'ummar a taron manema labarai ya ce "Idan gwamnatin ba za ta iya tabbatar da tsaro ba zamu kai ta kara zuwa majalisar dinkin duniya domin neman taimako".

Ya kara da cewar "Gwamnati ya kamata ta yi kokari ta kubutar da 'ya'yanmu saboda a yanzu bamu gani a kasa ba".

Wasu iyayen 'yan matan Chibok sun ce sun fara cire tsammanin sake ganin 'ya'yansu ganin yadda aikin cetonsu ke tafiyar hawainiya.

Kungiyoyi a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da yin gangamin matsa wa gwamnatin Najeriyar lamba, domin daukar matakin ceto 'yan matan, amma har yanzu babu amo ba labari.

Kungiyar Boko Haram ta haddasa mutuwar dubban mutane a Nigeria sannan ta yi barazanar sayar da 'yan matan Chibok din.