Ma'anar isharorin gwaggon biri

Hakkin mallakar hoto C HOBAITER
Image caption Birai na mafani da isharori don sadarwa a tsakaninsu

Masu bincike sun ce sun fassara ma'anar isharorin da gwaggon birai ke amfani da su don sadarwa a tsakaninsu.

A cewar masanan, gwaggon biran na aikewa juna kebantattun sakonni 19 ta hanyar amfani da isharori 66.

Masu binciken sun gano hakan ne ta hanyar bibiya da daukar hoton bidiyon wasu birai a Uganda, da kuma yin nazari a kan yadda aka yi amfani da wadannan isharori har sau 5,000.

An wallafa binciken ne dai a mujallar Current Biology.

Dokta Catherine Hobaiter, wacce ta jagoranci binciken, ta ce wannan ne kawai wani salo na sadarwa da aka taba samu a tsakanin dabbobi.

A cewarta, dan-Adam da gwaggon biri ne kawai ke da tsari na musayar bayanai ta hanyar aikewa da sako suna sane ga dan uwansu.

Ta shaida wa BBC cewa "Wannan ne abin ban mamaki ga isharorin na gwaggon biri. Su ne kadai wani abu mai kama da harsunan da dan-Adam ke amfani da su don cimma wata makamanciyar manufa".

Ko da yake binciken da aka gudanar a baya ya yi nuni da cewa kananan birai na iya fahimtar bayanai masu sarkakiya a kuka ko kururuwar wasu dabbobin, babu alamun da ke nuna cewa dabbobin na amfani da muryoyinsu suna sane don isar da sakonni.

Dokta Hobaiter ta kara da cewa wannan ne muhimmin bambancin da ke tsakanin kukan dabbobi da kuma ishara.

"Misali, idan ka dauki kofin shayi mai zafi, sai ka yi kururuwa sannan ka hura hannunka. Da haka zan fahimci cewa shayin na da zafi, amma kuma ba lallai ba ne ka yi niyyar sanar da ni hakan", inji ta.

A cewar masu binciken, wasu daga cikin isharorin gwaggon biri ma'anarsu karara take--wato ana amfani da ita ko da yaushe don isar da sako guda daya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gudanar da binciken ne a kan wata jama'a ta gwaggon biri a aka nada a bidiyo

Misali, idan gwaggon biri yana gutsurar ganyen bishiya, to ba ko tantama, yana nuni ne da cewa sha'awarsa ta motsa.

Amma wasu isharorin da dama masu harshen damo ne. Ana amfani da cafka, misali, don nuni da cewa "Bari", ko "Hau bayana", ko "Matsa can".

Wasu daga cikin hotunan bidiyon da aka dauka dai sun nuna karara abin da gwaggon biri ke nufi idan ya yi wata ishara.

A daya daga cikin hotunan, wata uwar gwaggon biri ta mika kafarta ga danta wanda ke 'yan koke-koke. Haka na nufin "Hau babu", kuma nan take dan ya haye bayanta suka fara tafiya.

"Babban darasin da wannan bincike ke koyarwa shi ne akwai wani jinsi da ke musayar bayanai masu ma'ana, ba mutane ne kadai ke da wannan tsari ba", inji Dokta Hobaiter.

Karin bayani