An kara kudin wuta da mai a Masar

Image caption Karin farashin mai kan jawo zanga-zanga a Masar, amma kawo yanzu ba a san yadda al'ummar za su mayar da martani ba.

Karin farashin wutar lantarki da albarkatun man fetur, ya fara aiki a kasar Masar, yayin da gwamnati ke shirin janye tallafin da take bayarwa a kansu.

Gwamnatin ta yi hakan ne, domin rage wagegen gibin da ake samu a kasafin kudinta, da nufin farfado da tattalin arzikin kasar wanda rikicin siyasa na shekaru ya balbalta.

An bayar da rahoton cewa farashin mai zai karu da kusan kashi 78 cikin dari , yayin da kudin wutar lantarki ake sa ran zai linka biyu cikin shekaru biyar masu zuwa.

Matsalar dauke wutar lantarki aba ce da ke neman zama ruwan dare a Masar din, inda jami'ai ke cewa, kudaden da gwamnati ke kashewa akan tallafin ya sa ,ake samun rashin kulawa da kuma kasa inganta fannin.