Google bai kyauta ba —Kakakin Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shafin matambayi-ba-ya-bata na Google na cire bayanai daga amsoshinsa idan aka bukaci hakan

Wani mai magana da yawun Hukumar Tarayyar Turai ya ce shawarar da kamfanin matambayi-ba-ya-bata na Google ya yanke ta cire wata kasidar BBC daga jerin amsoshin da yake bayarwa ba ta dace ba.

A karkashin wani hukunci da kotun Turai ta yanke ne, cewa mutum na da "hakkin a manta da shi" kamfanin ya cire wata rariyar likau zuwa ga kasidar ta Robert Peston, editan al'amuran tattalin arziki na BBC.

A cewar Ryan Heath, mai magana da yawun mataimakin shugaban Hukumar ta Tarayyar Turai, shi bai ga wani kwakkwaran dalili da zai kare muradun al'umma a wannan shawara ba.

Kasidar ta Robert Peston, wacce ya rubuta a watan Oktoban shekarar 2007, ta yi magana ne a kan bankin Merrill Lynch.

Ba a san wanda ya bukaci a cire kasidar ba, amma alamu na nuna cewa ba wanda aka ambata a kasidar ba ne, wato tsohon shugaban bankin na Merrill Lynch, Stan O'Neal.

A maimakon haka, bukatar ta danganci wani tsokacin masu karatu ne da aka yi a kasan kasidar.

Image caption Robert Peston ya ce kasidarsa ta dace da muradun al'umma

Wannan mataki da Google ya dauka dai na nufin daga yanzu idan wani ya nemi bayani dangane da mutumin da ya shigar da bukatar, to kasidar ba za ta fito a cikin amsoshin da Google zai bayar ba.

Amma idan aka nemi bayanin a wajen Turai, to kasidar za ta fito a cikin jerin amsoshin ba matsala.

BBC ta fahimci cewa Google na tankade da rairaya a kan rariyar likau fiye da 250,000 wadanda wasu mutane ke so a cire daga jerin amsoshin da shafin ke samarwa.

Wannan adadi ya kunshi bukatun da daidaikun mutane fiye da 70,000 suka shigar a tsakanin 29 ga watan Mayu da 30 ga watan Yuni.

Zuwa yanzu dai galibin wadannan bukatu sun samo asali ne daga Faransa, inda mutane 14,086 suka mika bukatarsu a wannan lokacin. Jamus kuma na bi mata da bukatu 12,678, yayinda Birtaniya ta rufa musu baya da bukatu 8,497.

Karin bayani